CBN Zai Fallasa Sunayen Bankunan Najeriya da Ke Harkallar Forex Ba Isa Ka’ida Ba, Za Ta Kunyata Su

HomeForex News

CBN Zai Fallasa Sunayen Bankunan Najeriya da Ke Harkallar Forex Ba Isa Ka’ida Ba, Za Ta Kunyata Su

Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi barazanar kakabawa bankunan da ke gudanar da hada-hadar kudaden waje takunkumiBabban bankin na CBN ya bayy

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi barazanar kakabawa bankunan da ke gudanar da hada-hadar kudaden waje takunkumi
  • Babban bankin na CBN ya bayyana cewa zai kai ziyarar ba-zata zuwa bankunan da ake zargi da laifin harkallar daloli ba tare da izini ba
  • Babban bankin ya ce zai kuma alanta suna da kuma kunyata bankunan kasuwanci da ke aikata irin wannan ta’asar

Najeriya – Babban bankin Najeriya (CBN) ya ba da gargadi game da matakin da za a iya dauka kan cibiyoyin hada-hadar kudi da ke da hannu wajen siyar da daloli ba bisa ka’ida ba ko kuma hada-hadar kudi ba tare da izini ba.

Gargadin ya biyo bayan koma bayan da darajar Naira ta Najeriya ta samu kan dala a kasuwannin da gwamnati ta amince da su da ma na bayan fage.

Folashodun Shonubi, mukaddashin gwamnan CBN ne ya sanar da hakan a lokacin da yake gabatar da wata lacca mai taken a Abuja, NairaMetrics ta ruwaito.

Yadda za a kama masu lalata Naira
Za a fallasa masu wulakanta darajar Naira | Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP, GettyImages
Asali: Getty Images

Shonubi ya jaddada muhimmancin daukar da tsauraran matakai na dakile safarar haramtattun kudade, tare da jaddada bukatar jagorantarsu ta hanyoyin da suka dace don bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasa gaba daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a [email protected]!

CBN zata fallasa tare da kunyata bankunan

A cewar jaridar The Guardian, gwamnan na CBN ya bayyana kafa wani kwamitin da zai aiwatar da ziyarar ba-zata ga cibiyoyin hada-hadar kudi da ake zargi da hannu a sayar da daloli ba tare da bin ka’ida ba.

Shonubi ya ce:

“Muna bukatar mu fallasa sunaye da kuma kunyata bankunan kasuwancin da ke da hannu cikin irin wannan munanan ayyuka.”

Gwamnan na rikon kwarya ya kara bayyana nakasuwar tsarin da ake amfani da shi wajen tura kudi a halin yanzu a kasar nan.

Ya yi kiyasin cewa tura kudade zuwa kasashen yankunan Afrika ta yamma daga kasashen waje na haifar da kashe kusan 8%-9% cikin dari cikin $100, adadin da ake ganin ya yi yawa.

Najeriya a daya daga kasashen da ‘ya’yanta ke yawan fuskantar matsaloli wajen hada-hadar kudaden waje, musamman dala.

Dalilin karyewar darajar Naira

A wani labarin, babban bankin Najeriya watau CBN ya ta’allaka faduwar Naira da aiko da kudi da ake yi daga kasashen ketare ba tare da hukuma ta sani ba.

A ranar Alhamis, Daily Trust ta ce Gwamnan bankin CBN na rikon kwarya, Folashodun Shonubi ya yi wannan bayani a makarantar tsaro a Abuja.

Folashodun Shonubi ya gabatar da takarda ga daliban makarantar da ke kwas na EIMC 16 mai taken aiko kudi daga ketare da cigaban tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

hausa.legit.ng

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: